1 Oktoba 2024 - 19:47
Iran IRGC: Mun Kai Hari Kan Sansanonin Sojojin Isra'ila Guda Uku A Kusa Da Tel Aviv

Dubban rokokinmu a shirye suke da a harba su idan muka ga wani motsi daga Isra'ila.

Bayan wannan harin Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin Sahayoniyya ta jaddada cewa Netanyahu da wasu ministocin Isra'ila sun boye a wani wuri mai tsaro a karkashin kasa a birnin Quds na tsawon sa'o'i da dama kuma ba su fito ba.

Har ila yau, wannan cibiyar sadarwa ta bayyana cewa, Yoav Gallant, ministan yaki, yana boye a karkashin kasa a Tel Aviv a wani gini mai kariya a hedkwatar ma'aikatar yaki saboda tsoron harin makami mai linzami na Iran. Wanda sojojin Isra'ila sun tabbatar da gazawarsu wajen katse makamai masu linzami na Iran

Ana haka sai Kakakin Sojin yahudawan sahyoniya ya ce: Mun katse wasu tsirarun makamai masu linzami na Iran ne kawai. Harin makami mai linzamin da Iran ta kai ya yi yawa matuka dangane da yawan makaman da harba shi.

Sanannen daga tushe mai nagarta ya tabbatar da cewa: Fiye da kaso 80% na makamai masu linzami sun isa gurin da aka nufa da su kai tsaye.

Wata majiya mai cikakken bayani ta ruwaito cewa sama da kashi 80% na makamai masu linzami sun afkawa wuraren da aka nufa a tashin farko.

Amurka tayi tarayya wajen tunkarar makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa yankunan Tel Aviv

Tashar talabijin ta sahyoniya ta 12 ta nakalto daga wani jami'in kasar Amurka ya bayyana cewa, Amurka na taka rawa wajen kakkabe makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa yankunan Isra’ila.

Pentagon: Sojojin ruwan Amurka sun harba makami mai linzami guda 12 don katse makaman da Iran ta harba kan Isra'ila, hare-haren na Iran "yayi tsamari sosai".

Sannan tashar talabijin ta Al-Najba ta kasar Iraki ta sanar da cewa an lalata hedikwatar Mossad gaba daya sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai.